logo

HAUSA

Mataimakiyar firaministan Sin ta jaddada cewa ya dace a hanzarta hana yaduwar cutar COVID-19 a Shanghai

2022-04-03 17:49:28 CMG Hausa

Memba a ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana mataimakiyar firaministan kasar Sin, Sun Chunlan ta tashi daga Jilin zuwa Shanghai jiya Asabar don ganewa idonta yadda ake gudanar da aikin dakile yaduwar cutar COVID-19, inda ta jaddada cewa, ya dace a tsaya ga muhimmiyar manufar dakile yaduwar cutar da zarar an gano ta, da daukar kwararan matakai ba tare da wani jinkiri ba, don aiwatar da manufofin kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis gami da na majalisar gudanarwa a zahirance.

Madam Sun ta ci gaba da cewa, ya kamata a gudanar da gwaji kan duk wani mutum dake da bukata, da killace wadanda suka kamu da cutar, tare kuma da ba su kulawa da magani. Sa’annan ya dace hukumomi daban-daban su shirya ma’aikatan lafiya da kayayyakin yaki da cutar yadda ya kamata, don taimakawa aikin dakile yaduwar cutar a Shanghai, ta yadda za’a samu nasarar yakar cutar tun da wuri. (Murtala Zhang)