logo

HAUSA

Rasha ta gano dakunan gwajin hada makamai da kwayoyin halittu da Amurka ke daukar nauyi a kewayen kasarta

2022-04-03 17:10:05 CMG Hausa

Gwamnatin Rasha ta yi zargin cewa, ta samu wasu bayanai dake nuna cewa, an gano wasu dakunan gwaje-gwaje domin aikin hada makamai da kwayoyin halittu a kewayen kasar Rashan, kamar yadda kakakin fadar Kremlin, Dmitry Peskov ya sanar a ranar Asabar.

Peskov, ya fada a yayin zantawa da tashar talabijin ta Belarus-24 TV cewa, karkashin wani shiri wanda helkwatar tsaron Pentagon ta dauki nauyi, an gina jerin dakunan gwaje-gwajen kwayoyin halitta a kewayen kasashen Rasha da Belarus, wadanda ba kawai suna lura da wasu kwayoyin halittu masu matukar hadari, da kwayoyin cutuka ba ne, har ma suna yin aiki kan shirye-shiryen samar da wasu nau’ikan makamai da kwayoyin halittu.

Ya ce, “A halin yanzu Amurka tana kokarin karkata hankalin duniya daga batun dakunan gwajin kwayoyin halittu, amma gaskiya zata yi halinta. Batun na damun Rasha da sauran kasashe.”

Dukkansu shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy, da na Amurka Joe Biden, sun fito fili sun musanta wannan ikirarin a jawabai na bainar jama’a da na shafukan sada zumunta na Facebook. Har ma sun yi ikirarin cewa wai Moscow ne ke shirin amfani da makaman da aka hada da kwayoyin halitta da kuma sinadarai masu guba kan Ukraine.

Babu wata kwakkwarar shaida dake gaskata ikirarin nasu. Majalisar dokokin Rasha tuni ta kafa hukumar bincikar dakunan gwaje-gwajen kwayoyin halittun da Amurka ke kula dasu a Ukraine.(Ahmad)