logo

HAUSA

Najeriya ta sassauta dokar amfani da takunkumin rufe fuska

2022-04-02 15:46:07 CMG Hausa

Hukumomi a Najeriya sun sanar a ranar Juma’a cewa, an sassauta dokokin amfani da takunkumin rufe fuska a duk fadin kasar, inda suka bayyana cewa, babu bukatar mutane su sanya takunkumin rufe fuskar a yayin da suke halartar budaddun wuraren taruwar jama’a, biyo bayan ci gaba da raguwar adadin masu kamuwa da annobar COVID-19 a kasar.

Ifedayo Adetifa, shugaban hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta kasar NCDC, ya fadawa manema labarau cewa, har yanzu, akwai bukatar a dinga amfani da takunkumin rufe fuskar yayin halartar taruka a rufaffun wurare ko kuma wurare masu matukar hadari.

Ya ce Najeriya ta aiwatar da matakai da dama na yaki da cutar COVID-19, da suka hada da mayar da hankali wajen ci gaba da sanya ido, da gwaje-gwajen cutar, da kuma yin riga-kafi, inda ya jaddada cewa, har yanzu amfani da takunkumin rufe fuskar ya kasance a matsayin muhimmiyar hanyar tabbatar da tsaron lafiyar al’umma.

A cewarsa, kyakkyawan amfani da takunkumin yana da matukar tasiri wajen yiwuwar rage yaduwar cutar a tsakanin mutanen da suka kamu da cutar, da kuma wadanda ake zaton sun kamu da cutar, kuma yana taimakawa wajen bada kariya ga mutanen dake da matukar hadarin kamuwa da cutar, da kuma masu fama da tsananin cutar.

Adetifa ya ce, karbar riga-kafin zai taimaka matuka tare da daukar karin wasu matakai, kamar sanya takunkumin rufe fuskar.(Ahmad)