logo

HAUSA

An shirya taron kiyaye tsaro ta kafofin bidiyo da wayar tarho a Beijing

2022-04-02 18:45:47 CMG Hausa

Bayan afkuwar hadarin jirgin saman kamfanin China Eastern Airlines MU5735 na "21 ga watan Maris ", shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ba da muhimmin umarnin gaggawa, inda ya bukaci a dauki dukkan matakan gudanar da ayyukan ceto, kana a gudanar da ayyukan bisa tsari mafi dacewa. Tare da gabatar da rahoton ayyukan gaggawa gami da gabatar da muhimman jawabai.

Domin aiwatar da hakikanin muhimmin umarnin da shugaba Xi ya bayar, hukumar kiyaye tsaro ta kasar Sin ta shirya taro ta kafofin bidiyo da wayar tarho a Beijing, kwanaki kadan da suka gabata, domin gudanar da tsare-tsaren da suka dace na samun cikakkiyar nasarar ayyukan kare haddura da sauke mihimman nauyi kuma cikakku a fannin ayyukan kare afkuwar haddura.(Ahmad)