logo

HAUSA

Shugaban Sin ya gana da shugaban majalisar zartaswar kasashen Turai da shugabar kwamitin kungiyar EU

2022-04-02 16:11:09 CMG Hausa

A jiya Jumma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban majalisar zartaswar kasashen Turai Charles Michel, da kuma shugabar kwamitin kungiyar tarayyar kasashen Turai (EU) Ursula von der Leyen, ta kafar bidiyo.

Yayin ganawar, shugaba Xi Jinping ya ce, shekaru 8 ke nan da ya gabatar da shawarar kafa dangantakar abokantaka bisa fannonin zaman lafiya, da neman karuwa, da yin kwaskwarima, da raya al’adu, tare da kasashen Turai cikin hadin gwiwa. Ya zuwa yanzu, kasar Sin ba ta canja matsayinta kan wannan batu ba. Yana mai cewa,“Daga shekarar 2021, ya zuwa yanzu, dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Turai ta sami sabon ci gaba sakamakon kalubalolin da suka fuskantarsu cikin hadin gwiwa, an kuma cimma sakamako masu kyau bisa hadin gwiwar bangarorin biyu. Abubuwan da suka faru sun nuna mana cewa, kasar Sin da kasashen Turai suna da moriyar bai daya, da tushe mai zurfi wajen habaka hadin gwiwa. Ba zai yiwu a iya warware matsaloli da kulubaloli yadda ya kamata ba, sai ta hanyar yin hadin gwiwa da mu’amala. Kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan manufarta game da kasashen Turai, kuma tana fatan kasashen Turai za su daidaita ra’ayoyinsu kan kasar Sin, da aiwatar da manufofin dake shafar kasar Sin cikin ’yanci, da yin hadin gwiwa da kasar Sin wajen inganta dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu kamar yadda ake fata.”

A nasu bangaren, shugaba Charles Michel da shugaba Ursula von der Leyen sun bayyana cewa, kasar Sin na da babban tasiri kan kasashen duniya, kasashen Turai suna matukar mayar da hankali wajen raya dangantakar dake tsakaninsu da kasar Sin. Tun da dadewa, aka kafa dangantakar taimakawa juna da cimma moriyar juna a tsakanin Turai da kasar Sin, kuma, bangarorin biyu suna dukufa wajen kare zaman lafiya da dangantakar cude-ni-in-cude-ka a tsakanin sassa daban daban. A halin yanzu, yana da muhimmanci wajen karfafa mu’amalar dake tsakanin kasashen Turai da kasar Sin. Kuma, sun sake jaddada matsayin kasashen Turai na kare manufar “kasancewar kasar Sin daya tak a duniya”, da kuma nuna fatan yin shawarwari tare da kasar Sin ba tare da rufa-rufa ba, domin ci gaba da raya dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu, da zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Turai a fannonin tattalin arziki da ciniki, zuba jari, raya makamashi, da neman bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba. Kana, sun nuna fatan karfafa hadin gwiwa domin fuskantar matsalar yaduwar annobar cutar COVID-19, da sauyin yanayi, da kuma kare nau’o’in hallitu, ta yadda za su ba da gudummawa a fannonin inganta zaman lafiyar duniya, da raya tattalin arzikin kasa da kasa, da kuma neman wadata cikin hadin gwiwa.

Bugu da kari, shugabanni sun yi musayar ra’ayoyi game da yanayin kasar Ukraine. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)