logo

HAUSA

UNHRC ta zartas da kudurin kare hakkin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma da al’adu da aka gabatar

2022-04-02 16:16:47 CMG Hausa

Jiya Juma’a 1 ga wata, hukumar kare hakkin dan adam ta MDD, ta kira taro karo na 49, inda aka zartas da kudurin ingiza kare hakkin raya tattalin arziki, da zamantakewar al’umma, da al’adu, da kuma kawar da rashin adalci, da kasashe 66 da suka hada da kasar Sin da Masar da Afirka ta Kudu da Bolivia suka gabatar.

Kudurin ya mai da hankali matuka kan koma bayan tattalin arzikin duniya sakamakon barkewar annobar COVID-19 a duniya, haka kuma ya yi kira ga kasashen duniya daban daban da su yi amfani da dukkan albarkatunsu domin ingiza kare hakkin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma da al’adu, tare kuma zuba jari a fannonin kiwon lafiyar jama’a, da ba da ilmi, da ba da tabbacin zamantakewar al’umma, da kuma samar da abinci.

Zaunannen wakilin kasar Sin dake Geneva, Chen Xu, ya yi bayani kan daftarin kudurin a madadin kasashen da suka gabatar da kudurin, inda ya bayyana cewa, annobar COVID-19 ta haifarwa kasashen duniya, musamman ma kasashe masu tasowa kalubalen da ba a taba ganin irinsa a baya ba, lamarin da ya nuna muhimmancin ingiza kare hakkin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma da kuma al’adu. (Jamila)