logo

HAUSA

Ma’aikatar wajen Sin: Sin da EU sun cimma ra’ayi daya kan fannoni da dama

2022-04-02 16:24:10 CMG Hausa

Yau Asabar 2 ga wata, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta kira taron manema labarai, inda aka yi bayani kan ganawa karo na 23 a tsakanin shugabannin kasar Sin da kungiyar tarayyar kasashen Turai wato EU.

Shugaban hukumar kula da harkokin kasashen Turai na ma’aikatar harkokin wajen kasar Wang Lutong, ya yi tsokaci yayin taron cewa, an sake shirya ganawar shugabannin Sin da EU ta shekara shekara, bayan shekaru biyu da suka gabata, ana iya cewa, ganawar ta kasance cudanya mafi muhimmanci a tsakanin shugabannin sassan biyu wato Sin da EU a bana, ta haifar da kyakkyawan sakamako, har ma sassan biyu sun cimma ra’ayi daya a fannoni da dama.

Jami’in ya kara da cewa, ganawar ta nuna cewa, sassan biyu suna da aniyar yin kokari tare domin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin duniya, tare kuma da sa kaimi kan farfadowar tattalin arzikin duniya.

Ban da haka kuma, sassan biyu wato Sin da EU su ma sun yi musanyar ra’ayi kan batutuwan kasa da kasa da suka jawo hankalinsu duka, misali rikicin kasar Ukraine, inda suka bayyana cewa, ya dace a daidaita rikicin ta hanyar tattaunawa. (Jamila)