logo

HAUSA

Xi Jinping ya bayyana cikakken ra’ayinsa kan yadda za a dakile rikicin Ukraine

2022-04-02 16:43:55 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da shugaban majalisar gudanarwar kungiyar tarayyar Turai Charles Michel, da shugabar hukumar gudanarwar kungiyar, Ursula von der Leyen, a Beijing, da yammacin ranar 1 ga watan Afrilu.

Yayin ganawar, Xi Jinping, yayi cikakken bayani kan ra’ayoyi daban-daban game da yadda za a warware rikicin Ukraine a bisa yanayin da ake ciki a halin yanzu, na farko ya ce, ya zama dole a sa kaimi wajen lalibo hanyoyin zaman lafiya, da yadda za a daga matsayin tattaunawar sulhu. Na biyu, a yi kokarin kandagarki na hana karuwar girman matsalolin masu bukatar tallafin jin kai. Na uku, a yi kokarin gina cikakken tsarin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a Turai da ma nahiyoyin Turai da Asiya. Na hudu, ya ce dole ne a yi kokarin dakile hanyoyin da suke haifar da barkewar karin tashe-tashen hankulla.(Ahmad)