logo

HAUSA

Sin za ta maida martani kan wasu jami’an Amurka

2022-04-01 10:41:04 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce kasar sa za ta aiwatar da matakan hana wasu jami’an kasar Amurka Visa, wadanda suka kirkiri karairayi, masu alaka da zargin keta hakkokin bil adama, tare da sa kaimin sanya takunkumi ga kasar Sin, da illata moriyar kasar.

Wang ya bayyana hakan ne, a yayin taron manema labarai na jiya Alhamis, bayan da Amurka ta bayyana aniyar sanyawa wasu jami’an kasar Sin takunkumin hana Visa, bisa fakewa da zargin keta hakkin bil adama.

Jami’in ya kara da cewa, Sin ba za ta taba amincewa da irin wadannan matakai na keta dokokin kasa da kasa, da ka’idojin cudanyar kasashen duniya ba.

Don haka dai, Sin ta amince da daukar matakin ramuwar gayya, domin tabbatar da kare ‘yancin mulkin kan ta, da tsaro, da ci gaban moriyar ta, da kuma kare halastattun hakkokin jami’an ta. Za ta kuma ci gaba da bin dokokin ta masu nasaba da kariya daga takunkumai daga ketare.    (Saminu)