logo

HAUSA

Sin ta bukaci NATO da ta yi tunani kan rawar da take takawa a rikicin Ukraine

2022-04-01 19:42:13 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yayin taron manema labaru na yau da kullum Jumm’ar nan cewa, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bukaci kungiyar tsaro ta NATO, da ta yi tunani kan irin rawar da take takawa a rikicin kasar Ukraine da kuma tsaron nahiyar Turai kanta.

Zhao ya bayyana lokacin da aka tambaye shi game da batun da Rasha ta gabatar kan fadada kungiyar NATO cewa, duniya ba ta bukatar wani sabon yakin cacar baki, kuma ita ma Turai ba ta bukatar hakan.(Ibrahim)