logo

HAUSA

Jakadan Sin a Najeriya ya gana da ministan noma da cigaban karkara na Najeriya

2022-04-01 12:36:02 CMG Hausa

 

Jiya Alhamis 31 ga watan Maris, Jakadan kasar Sin da ke Tarayyar Najeriya Cui Jianchun, ya gana da ministan noma da cigaban yankunan karkara na Najeriya Mohammed Abubakar.

Yayin tattaunawar tasu Jakada Cui ya bayyana cewa, ayyukan gona muhimmin fanni ne na hadin kan kasashen biyu, wanda ke kunshe da sirrin cigaba, duba da yawan al’ummun kasashen biyu.

Kasar Sin na son inganta hadin gwiwa tare da Najeriya a wannan fanni, kamar sa kaimi ga raya ayyukan shuka ciyayin Juncao, da ciyayin magungunan gargajiyar Sin, da ma fasahar amfani da haske wajen kashe kwayoyin cuta, a kokarin amfanar da dumbin al’umma, da ma ciyar da hadin kan kasashen biyu gaba ta fuskar ayyukan gona.

A nasa bangaren, Mr. Mohammed Abubakar ya bayyana cewa, noma tushe ne na arziki. Kuma Sin ta samu manyan nasarori a fannonin tabbatar da samar da isasshen hatsi, da sa kaimi ga zamanintar da sha’anin noma. Don haka Najeriya ke fatan yin kokari tare da Sin, wajen habaka fannonin hadin kansu, da ingiza aiwatar da ayyuka masu nasaba da hakan cikin hanzari, ta yadda za a samu karin sakamakon azo a gani, bisa hadin kan bangarorin biyu.   (Kande Gao)