logo

HAUSA

Sin: Wajibi ne mu martaba ka'idodin gama gari kan yaki da COVID-19

2022-04-01 19:31:21 CMG Hausa

A yammacin yau ne kwamitin yaki da annobar COVID-19 na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya gudanar da taron manema labarai. A yayin taron, mai magana da yawun hukumar lafiya ta kasar Mi Feng, ya ce kamata ya yi a kiyaye baki dayan manufofin yaki da annobar COVID-19 a ko da yaushe, kana a dakile yaduwar cutar nan da nan.

Kamar yadda aka gabatar a yayin taron, daga ranar 1 zuwa 31 ga watan Maris, an samu rahoton mutane 103,965 da suka kamu da cutar a duk fadin kasar, wanda ya shafi larduna 29.(Ibrahim)