logo

HAUSA

Za a wallafa muhimmiyar makalar shugaba Xi game da noma da raya karkara

2022-04-01 11:05:06 CMG Hausa

A yau Juma’a ne mujallar “Qiushi” ta kwamitin kolin JKS, za ta wallafa muhimmiyar makalar shugaban kasar Sin Xi Jinping, wadda ta yi cikakken bayani kan batutuwan da suka shafi harkar noma da yankunan karkara, da zamantakewar al’ummu dake zaune a kauyuka.

A cikin makalar, Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin da gwamnatin sa ke dorawa kan harkar noma da yankunan karkara, da zamantakewar al’ummu dake zaune a kauyuka, yana mai tabbatar da aniyar JKS, da ma daukacin al’ummar Sinawa, ta kara azama wajen bunkasa karkara.

A cewar shugaban, aiki mafi wahala da daraja, dangane da gina al’umma ta zamani mai bin salon gurguzu, ya ta’allaka ne ga nasarar raya karkara.

Makalar ta kara da cewa, Sin za ta ci gaba da dora muhimmancin gaske, kan aiwatar da manufofin samar da isasshen abinci, don haka akwai bukatar aiwatar da matakai tsaurara na kare filayen noma, da gaggauta cimma nasarori a fannin raya ginshikan fasahohin raya ayyukan gona. (Saminu)