logo

HAUSA

NED ta Amurka tana aikata mugunta da sunan dimokradiyyar karya!

2022-04-01 19:19:21 CMG Hausa

Kwanan nan ne, shugaban gidauniyar tallafin demokradiyya (NED), Dimon Wilson, ya jagoranci wata tawaga da ta kai ziyara yankin Taiwan na kasar Sin, inda ya fito karara ya bayyana cewa, shi ne ya haifar da "juyin juya hali" a duniya. Wannan muguwar kungiya ta yi tattaki zuwa kofar kasar Sin, don yin aiki da sunan demokuradiyya, a wani yunkuri na haddasa "juyin juya hali". Yadda take furta kalamai da ayyukanta, zai sa ta ci mummunan tura!

Kowa ya san wace ce gidauniyar tallafin demokraɗiyya ta kasa. Tun bayan kafuwar wannan kungiya mai zaman kanta da gwamnatin Amurka ke daukar nauyinta, da nufin tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran kasashe da kuma gurgunta halastattun gwamnatocin wasu kasashe. (Ibrahim)