logo

HAUSA

Nasarar kasar Sin ta rage talauci ta zama misali ga duniya

2022-03-31 20:47:24 CMG Hausa

Wani rahoton da aka fitar Alhamis din nan ya nuna cewa, nasarorin da kasar Sin ta cimma wajen rage talauci, sun kasance abin koyi ga sauran kasashen duniya.

Ragoton wanda ma'aikatar kudi da cibiyar bincike ta majalisar gudanarwar kasar Sin da kuma bankin duniya suka fitar cikin hadin gwiwa, ya bayyana cewa, a cikin shekaru arba'in da suka gabata, kasar Sin ta yi nasarar fitar da kusan mutane miliyan 800 daga kangin talauci, bisa mizanin da ake amfani da shi, wajen auna talauci kan dalar Amurka 1.9 da kowane mutum ke iya samu a kowace rana a fadin duniya.(Ibrahim)