logo

HAUSA

Wang Yi ya jagoranci taron ministocin harkokin wajen kasashe makwabtan Afghanistan karo na 3

2022-03-31 19:30:10 CMG Hausa

Yau ne, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya jagoranci taron ministocin harkokin waje na kasashen dake makwabtaka da kasar Afghanistan karo na uku a birnin Tunxi na lardin Anhui. A jawabin da ya gabatar a madadin bangaren kasar Sin, Wang Yi ya ba da shawarar cewa, dukkan bangarorin sun goyi bayan kasar Afghanistan, kan hanyar samun dogaro da kai, da wadata, da ci gaba, da samun ci gaba cikin lumana.

Taron ya kuma fitar da sanarwar hadin gwiwa ta taron ministocin harkokin waje game da kasar Afghanistan karo na uku da kuma shirin Tunxi na kasashen dake makwabta da Afghanistan kan tallafawa wajen sake gina tattalin arzikin Afghanistan da hadin gwiwa a zahiri.

Bayan kammala taron, Wang Yi ya bayyana ra'ayin da aka cimma a yayin taron, a madadin dukkan bangarorin da suka halarci taron, na farko, ya jaddada mutunta 'yancin kai na kasar Afghanistan, da goyon bayan al'ummar kasar su tantance makomar kasarsu da kansu.

Dukkanin bangarorin da suka halarci taron, sun bukaci Amurka da kasashen yammacin duniya, da su gaggauta sauke nauyin da ke wuyansu na sake gina kasar Afghanistan, da ci gaban kasar da kuma mayar da dukiyoyin al'ummar kasar ba tare da bata lokaci ba.

A wannan rana, Wang Yi ya gana da wakilan taron shawarwari na "Sin-Amurka-Rasha+" kan batun kasar Afghanistan, ciki har da wakilai na musamman da wakilan kasashen Sin da Amurka da Rasha da Pakistan. (Ibrahim)