logo

HAUSA

Rukunin masana'antun sojan Amurka: Hada kai don samun moriyar yaki

2022-03-31 19:13:04 CMG Hausa

Yau sama da wata guda ke nan da barkewar rikici tsakanin kasashen Rasha da Ukraine, kuma har yanzu ana ci gaba da gwabza fada. Fadan ba kawai ya yi sanadin rayuka da jikkatan sojoji da fararen hula na kasashen biyu ba, har ma ya sa miliyoyin 'yan kasar Ukraine zama 'yan gudun hijira. A matsayin wadda ta tayar da rikici tsakanin kasashen Rasha da Ukraine, Amurka ta ci gaba da "mika wukake" ta bayan fage, wanda ke da alaka da yanayi "rukunin masana'antun sojanta". Wannan hadin gwiwa ne na kut-da-kut tsakanin sojojin Amurka, da masana'antu, da gwamnati, da majalisa, da sauransu, da kuma hada kai da masana, da kafofin yada labarai, da dai sauransu, don kafa kungiyoyi masu ra’ayi iri daya. Wannan kungiya ta ci gaba da haifar da "makiya" a sassan duniya, suna kuma samun moriyar yaki mai tarin yawa, ta hanyar tayar da rikice-rikice a wasu kasashe, kuma rikicin kasashen Rasha da Ukraine shi ne ganima na baya-bayan da wannan gungu ya samo. (Ibrahim)