logo

HAUSA

Wang Yi ya shugabanci ganawar ministocin harkokin wajen kasashen Sin da Afghanistan da Pakistan

2022-03-31 14:15:55 CMG Hausa

 

Jiya Laraba 30 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya shugabanci taron ganawar ministocin harkokin wajen kasashen Sin da Afghanistan da Pakistan, wanda ya samu halartar ministan harkokin wajen kasar Pakistan Moeen Qureshi, da Amir Khan Mottaki, mukaddashin ministan harkokin wajen gwamnatin rikon kwarya ta Afghanistan.

Yayin ganawar da aka yi a garin Tunxi na lardin Anhui dake gabashin kasar Sin, Wang Yi ya bayyana cewa, a yanayin da ake ciki yanzu, ya kamata Sin da Afghanistan da Pakistan, su sake kaddamar da tsarin hadin kansu, a kokarin sa kaimi ga hadin gwiwarsu a fannonin siyasa da cigaba da tsaro, bisa manufofin girmama juna, da yin shawarwari cikin daidaito, da cimma muradun juna don samun nasara tare.

Qureshi da Mottaki, sun darajta muhimmiyar ma’anar kiran wannan taron ganawa, da ma taron ministocin harkokin wajen kasashe makwabtan kasar Afghanistan, inda Qureshi ya nuna cewa, kasar Pakistan na goyon bayan Afghanistan wajen kara tuntubar waje, kana tana son taimakawa Afghanstan wajen kyautata zaman rayuwar al’ummar kasar, da neman samun karin fahimta da goyon baya.

A nasa bangaren, Mottaki ya ce, kasar Afghanistan ta sake yin alkawari ga Sin da Pakistan da ma duk duniya, cewar sam ba za ta yarda da ’yan ta’adda, su lahanta muradun sauran kasashe, da ’yan kasashen waje a cikin kasar ba. (Kande Gao)