logo

HAUSA

Antony Blinken ya kammala ziyara a gabas ta tsakiya

2022-03-31 10:30:37 CMG Hausa

A jiya Laraba ne, sakataren wajen Amurka Antony Blinken, ya ziyarci kasar Algeria, a matsayin zangon karshe na ziyarar da ya kai wasu kasashen gasar ta tsakiya, inda ya gana da shugaban kasar Abdelmadjid Tebboune, da tsohon firaministan kasar Ramtane Lamamra.

Yayin ziyarar wuni guda a birnin Algiers, Blinken ya zanta da jagororin gasar, game da batutuwan da suka shafi tsaro, da hadin gwiwar raya tattalin arziki, da kuma halin da ake ciki game da rikicin Rasha da Ukraine, wanda a cewar sa ya haifar da matsalar hauhawar farashin abinci da makamashi.

Da yake jawabi ga manema labarai a ofishin jakadancin Amurka dake birnin Algiers, Mr. Blinken ya ce tsaro, da yaki da ta’addanci, na sahun gaba cikin manyan manufofin raya dangantakar diflomasiyya tsakanin Amurka da Algeria. Ya kuma ce Algeria na ci gaba da taka muhimmiyar rawa, a fannin shawo kan rikicin kasashen Mali da Libya, yayin da kasashen biyu suka dulmiya cikin danbarwar siyasa, bayan da sassan da ba sa ga maciji da juna suka gaza cimma yarjejeniya, kan yadda za a gudanar da zabukan shugabannin kasashen.

Game da matsalolin dake addabar yankunan yammacin Sahara kuwa, Blinken ya ce "Matsayar mu ba ta sauya ba; muna tabbatar da cikakken goyon bayan mu ga wakilin musamman na MDD, kan kwazon sa na ganin an warware halin tashin hankali da yankin ke ciki".

Kafin Algeria, Mr. Blinken ya ziyarci yankin Falasdinu, da kasashen Isra’ila da Morocco.  (Saminu)