logo

HAUSA

An kira taron ministocin harkokin wajen kasashe makwabtan Afghanistan

2022-03-31 14:12:32 CMG Hausa

 

A safiyar yau Alhamis 31 ga wata, an kira taro karo na uku, na ministocin harkokin wajen kasashe makwabtan Afghanistan a garin Tunxi da ke lardin Anhui na kasar Sin. Taron da ya gudana a karkashin jagorancin ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya samu halartar ministocin harkokin waje, da wakilai daga kasashen Pakistan, da Iran, da Rasha, da Tajikistan, da Turkmenistan da Uzbekistan. Inda bangarori daban daban suka yi musanyar ra’ayoyinsu, da ma daidaita matsayinsu kan batutuwan dake shafar aikin sa kaimi ga samun zaman karko a Afghanistan, da tallafa wa al’ummar kasar da dai sauransu.

Bayan taron, minista Wang Yi zai jagoranci taron tattaunawa, mai taken “Afghanistan da makwabtanta”, inda za a gayyaci Amir Khan Mottaki, mukaddashin ministan harkokin wajen gwamnatin rikon kwarya na Afghanistan, da ministocin harkokin wajen kasashen Indonesiya, da Katar don su halarci taron. (Kande Gao)