logo

HAUSA

Dai Bing: Ci gaba da kakaba takunkumai kan rikicin Ukraine ba zai haifar da da mai ido ba

2022-03-30 10:49:42 CMG Hausa

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Dai Bing, ya yi kashedin cewa, sanya takunkumai barkatai, sakamakon rikicin kasar Ukraine, zai haifar da sabbin matsalolin jin kai ga al’ummun duniya, ciki har da kamfar makamashi, da abinci, da tabarbarewar hada hadar cinikayya, da tattalin arziki, da kasuwanin hannayen jari.

Jami’in ya kara da cewa, kasashe masu tasowa, wadanda su ne mafi rinjaye cikin jimillar kasashen duniya, ba su da hannu cikin wannan yaki, don haka bai kamata a ja su cikin sa ba. Dai Bing ya kara da cewa, ya kamata sassan kasa da kasa su kara ingiza bukatar komawa teburin shawara tsakanin Rasha da Ukraine, har a kai ga cimma kyakkyawan sakamako, da dawo da yanayin zaman lafiya.

Ya ce Sin za ta ci gaba da aiki tukuru, wajen saukaka yanayin da ake ciki, tare da ba da tallafin da ya dace, na shawo kan rigimar sassan biyu.  (Saminu)