logo

HAUSA

Ministan wajen Sin ya tattauna da babban jami’in diflomasiyyar Turai

2022-03-30 10:41:06 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya halarci taron tattaunawa da babban wakilin kungiyar tarayyar Turai EU mai kula da sashen hulda da kasashen waje, Josep Borrell, ta kafar bidiyo, Wang ya halarci tattaunawar ne daga birnin Tunxi, dake lardin Anhui na gabashin kasar Sin.

Wang Yi ya ce, Sin da EU, manyan bangarori biyu ne a harkokin kasa da kasa, ya dace su ci gaba da kyautata dabarun tuntubar juna, su inganta kyakkyawar fahimtar dake tsakaninsu, kuma su ci gaba da fadada hadin gwiwar dake tsakaninsu, kana su hada gwiwa domin yin aiki tare wajen magance manyan kalubaloli daban daban dake tinkarar duniya.

Wang ya kuma bukaci bangarorin biyu su yi kyakkyawan shirin tsara muhimmiyar hulda a tsakaninsu don samun nasarar aiwatar da dabarun hadin gwiwa a tsakanin bangarorin biyu domin isar da wani muhimmin sako ga duniya.

Borrell a nasa bangaren ya bayyana cewa, EU a shirye take ta ci gaba da daukar matakan kyautata huldar dake tsakaninta da kasar Sin. Ya kuma jaddada aniyar EU na kiyaye manufar Sin daya tak a duniya. Yana mai cewa, EU da kuma dukkan mambobin kasashen kungiyar EU ba za su taba kaucewa daga kan wannan matsayi ba.

Game da batun rikicin Ukraine, Borrell ya ce, rikicin ya haifar da mummunan tasiri ga EU da duniya baki daya, kuma EU ta bukaci a gaggauta tsakaita bude wuta.

A nasa bangaren, Wang Yi ya ce, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da al’ummar kasa da kasa domin ci gaba da yin kira a tabbatar da tsakaita bude wuta, da shiga tattaunawar zaman lafiya, da kaucewa karuwar girman matsalar ayyukan jin kai bil adama, da kuma bude kofar tabbatar da zaman lafiya. (Ahmad)