logo

HAUSA

Shin Amurka ce ke aiwatar da gwajin halittu na harkar soja a Ukraine?

2022-03-30 15:32:00 CMG Hausa

Kwanan baya, ma’aikatar harkokin tsaron kasar Rasha ta sanar da gano shirin gwajin halittu na harkar soja a kasar Ukraine, wanda kasar Amurka ta samar da taimakon kudin gudanarwa. Kuma, bisa shaidun da kasar Rasha ta fidda, a halin yanzu, ana nazarin makamai na halitta a dakunan gwaje-gwajen.

A bangaren kasar Amurka kuma, mataimakiyar ministan harkokin waje Victoria Nuland ta amince cewa, kasar Amurka tana da dakunan gwaje-gwajen nazarin ilmin halittu a kasar Ukraine, kuma, tana yin hadin gwiwa da kasar Ukraine, domin hana shigar kasar Rasha cikin kasar Ukraine.

Haka kuma, an fidda labarai cewa, kasar Amurka ta taba goge wasu takardu a ofishin jakadancin kasar Ukraine, amma, ta mayar da wadannan takardu bayan wasu lokuta. Kuma, bisa binciken da aka yi, an tabbatar da cewa, an canja wasu bayanai daga cikinsu.

A shekarar 2020, dan majalisar jam’iyyar adawa ta kasar Ukraine Viktor Medvedchuk ya taba bayyana cewa, bayan kasar Amurka ta ba da taimakon kudi wajen kafa dakunan gwaje-gwaje a kasar Ukraine, sau da dama, an gamu da matsalolin yaduwar cututtuka da ba a iya gano asalinsu ba.

Dangane da wadannan tambayoyin da aka yi wa kasar Amurka, kasar ba ta yi bayani yadda ya kamata ba, balle ma ta yarda da gamayyar kasa da kasa su yi bincike kan wannan batu a fili. Maimakon haka, sai ta ci gaba da zargin kasashen da suka yi mata wannan tambaya, kamar kasar Rasha da sauransu. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)