logo

HAUSA

Sabon zagayen cutar COVID dake barazana ga yara Amurkawa

2022-03-30 15:40:04 CMG Hausa

Yanzu haka, wata guda ke nan da kasar Birtaniya ta fara fuskantar barazanar yaduwar sabon nau’in cutar COVID-19. Ko da yake, hasarar rayukan da ake samu bai kai girman wanda annobar COVID-19 ta haifar a lokutan baya ba. Amma hakan ba yana nufin al’amarin karami ba ne.

Sabon zagayen cutar a Birtaniya, wanda ya kasance mafi girma a fadin nahiyar Turai da Asiya wanda nau’in cutar BA.2, wani bangare na cutar COVID-19 sabon nau’in Omicron, wanda yake matukar shafar kananan yara.

Wadannan al’amurra ba kawai sun kebanta ga kasar Birtaniya kadai ba ne, sai dai ya shafi sauran kasashe, da suka hada da Amurka, wadanda za su iya fuskantar mummunan tasirin tsananin cutar kan kananan yara, da zarar nau’in cutar ta BA.2 ya ci gaba da fantsama. (Ahmad)