logo

HAUSA

Cika shekaru 50 da kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Burtaniya kyakkyawar dama ce ta karawa yammacin duniya fahimtar kasar Sin

2022-03-30 11:13:22 CMG Hausa

Bana, shekaru 50 ke nan da kulla huldar diflomasiyya a matsayin jakadanci tsakanin kasar Sin da kasar Burtaniya. Dangane da wannan batu, shugaban cibiyar nazarin harkokin kasar Sin a jami’ar Oxford Rana Mitter ya bayyana cewa, kasar Sin da kasar Burtaniya, sun ba da muhimmiyar gudummawa, wajen fuskantar kalubalolin dake gaban dukkanin bil Adama, bisa kyakkyawan hadin gwiwar da suka yi a fannonin raya kasa da kasa, da warware matsalar sauyin yanayi. Ya ce,“A gani na, kasar Sin da kasar Burtaniya, sun cimma matsayi daya wajen daukar karin nauyin raya kasa da kasa, musamman ma a fannin rage yawan hayaki mai dumama yanayin duniya. Domin suna da fasahohi masu kyau na bunkasa tattalin arziki, ta yadda za su habaka hadin gwiwar dake tsakaninsu yadda ya kamata. Shi ya sa, a lokacin da muke taya murnar cika shekaru 50 da kafuwar huldar diflomasiyya a matsayin jakadanci tsakanin kasashen biyu, muna iya tunawa da muhimmiyar rawar da kasashen biyu suka taka, wajen raya duniyarmu cikin hadin gwiwa.”

Ban da haka kuma, shehun malami Rana Mitter ya bayyana cewa, a halin yanzu, kasar Sin na yin karin tasiri ga kasashen duniya, kuma, cika shekaru 50 da kafuwar huldar diflomasiyya a matsayin jakadanci tsakanin Sin da Burtaniya, zai iya kasancewa kyakkyawar dama ta kara fahimtar al’ummomin yammacin duniya kan kasar Sin. Ya kuma nuna fatan cewa, za a sami karin matasan Burtaniya dake son koyon Sinanci, yayin da suke kara saninsu game da tarihi, da al’adu, da sauran harkoki game da kasar Sin. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)