logo

HAUSA

Xi ya dasa itatuwa tsawon shekara 10 a matsayin shugaban kasa

2022-03-30 20:56:50 CMG Hausa

Yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya dasa itatuwa a nan birnin Beijing, inda ya cika shekaru 10 cif yana halartar wannan aiki, a matsayinsa na babban jagoran aikin dashen itatuwa na shekara shekara a fadar mulkin kasar Sin.

Shugaban ya kuma jaddada bukatar ci gaba da kokarin da ake yi na karewa da dawo da tsarin muhalli da kuma cimma muhimman abubuwan inganta muhalli. (Ibrahim)