logo

HAUSA

Nijeriya ta kafa kwamitin binciken manufofin ciniki

2022-03-30 12:25:14 CMG Hausa

Kwanan baya, gwamnatin tarayyar Nijeriya ta sanar da kafa kwamitin binciken manufofin ciniki, wanda ke kunshe da sashen zuba jari, da cinikin masana’antu na tarayyar Nijeriya, da ofishin shawarwarin ciniki na kasar, da kuma babbar hukumar kwastan ta Nijeirya da sauransu.

A yayin bikin kaddamar da kwamitin, ministan harkokin ciniki da zuba jari na kasar Adeniyi Adebayo ya bayyana cewa, babban makasudin kafuwar kwamitin shi ne, raya tattalin arziki da rage talauci, ta hanyar raya ciniki tsakanin kasa da kasa, da kuma aikin zuba jari. Ya ce, kwamitin zai sake daidaita manufofin ciniki, domin tabbatar da cewa, sabbin manufofin kasar za su dace da tsarin ciniki da tattalin arziki na duniya, musamman ma, hanyar aiwatar da tunanin yadda tsarin tattalin arziki da ciniki suka sauya, bayan matsalar kudi ta duniya ta shekarar 2008, da kuma gabanin matsalar yaduwar cutar COVID-19 cikin kasashen duniya a halin yanzu. (Maryam)