logo

HAUSA

An gudanar da taron karawa juna sani mai taken zamanintar da hanya mafiya dacewa da tsarin jam’iyyun siyasar Sin da Afrika

2022-03-30 14:03:38 CMG Hausa

A ranar Talata, sashen hulda da kasashen waje na kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin CPC, ya gudanar da taron karawa juna sani ta kafar bidiyo mai taken: “zamanintar da hanya mafi dacewa da tsarin jam’iyyun siyasar kasashen Sin da Afrika.” Shugabannin jam’iyyun siyasa 17 daga kasashen Afrika 16, da manyan shugabannin kafafen yada labarai na wasu daga cikin kasashen, da suka hada da Solomon Tsenoli, mamban kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta Afrika ta kudu kana mataimakin kakakin majalisar dokokin kasar, da John Akpan Udoedehe, babban sakataren kwamitin rikon kwaryar jam’iyyar (APC), na daga cikin mahalarta taron.

Song Tao, shugaban sashen hulda da kasa da kasa na CPC, ya bayyana cikin jawabinsa cewa, CPC a shirye take tayi aiki tare da jam’iyyun siyasar Afrika domin aiwatar da muhimman yarjejeniyoyin da shugabannin bangarorin biyu suka cimma, da karfafa musayar ra’ayoyi da hadin gwiwa, da kuma bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen gina ingantacciyar makomar alummun Sin da Afrika.

Mahalarta daga kasashen Afrika, sun yi matukar yabawa nasarorin da jam’iyyar CPC ta cimma na kokarin zamanantar da hanyoyi mafi dacewa da yanayin kasar Sin, tare da kafa kyakkyawan abin koyi ga kasashen Afrika. Sun kuma bayyana aniyarsu na zurfafa hadin gwiwa da CPC a fannoni daban-daban, da daga matsayin ci gaban huldar Sin da Afrika. (Ahmad)