logo

HAUSA

Mazauna Tibet Sun Yi Murnar Cika Shekaru 63 Da ’Yantar Da Miliyoyin Bayi Manoma

2022-03-29 10:55:51 CMG Hausa

Kwanan baya, ’yan kabilu daban daban mazauna jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin, sun sanya kyawawan tufafi tare da yin wake-wake da raye-raye, domin murnar cika shekaru 63 da ’yantar da miliyoyin bayi manoma a Tibet.

A shekarar 1959, ’yan kabilu daban daban na Tibet sun kaddamar da wani gangamin yin gyare-gyare ta fuskar dimokuradiyya a wurin, inda aka ’yantar da miliyoyin bayi manoma, wadanda suka samu ’yanci. Da zummar amsa kiran mazauna Tibet miliyan 2 da dubu 800, da kuma bukatunsu, hukumar kafa dokar jihar Tibet ta ayyana ranar 28 ga watan Maris na kowace shekara, a matsayin ranar tunawa da ’yantar da miliyoyin bayi manoma na Tibet. (Tasallah Yuan)