logo

HAUSA

Amurka da NATO sun yi gwaje-gwajen kwayoyin halittu a kasar Ukraine

2022-03-29 15:52:41 CMG Hausa

ma’aikatar tsaron kasar Rasha, ta fitar da wasu kundin bayanai da ta samu, daga wasu jami’ai masu aiki a dakin gwaje-gwajen kwayoyin halittu dake kasar Ukraine. Bayanan sun fallasa binciken da Amurka da kawayenta na kungiyar tsaro ta NATO ke yi, masu nasaba da kwayoyin cuta na yaki, ciki har da dabarun yada kwayoyin cutar murar tsuntsaye mai matukar hadari, ta hanyar tsuntsaye, da nau’o’in kwayoyin bacteria da na virus, wadanda ka iya yaduwa daga jemagu zuwa mutane. 

Kaza lika bayanan sun nuna cewa, an riga an yi amfani da wasu sassan jini masu yawa, kuma irin wadannan gwaje-gwaje da ake yi a Ukraine, sun yi kama da wanda kasar Japan ta yi a cibiyar “Unit 731”, yayin yakin duniya na II.

Kafar IOL, daya daga kafafen watsa labarai ta yanar gizo dake Afirka ta kudu, ta fitar da rahoto mai nasaba da hakan, inda ya ce “Dole mu yi taka tsan tsan, game da hadarin dake tattare da irin wadannan dakunan gwaje gwaje da ba a tantance su ba, dake sassan duniya daban daban”. (Saminu Hassan)