logo

HAUSA

Rahoton da Amurka ta fitar cike yake da tunanin yakin cacar baki da fito na fito

2022-03-29 19:47:18 CMG Hausa

Game da abubuwan da suka shafi kasar Sin dake kunshe cikin rahoton dabarun tsaron kasa da Amurka ta fitar, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Wang Wenbin, ya yi nuni a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa Talatar nan cewa, rahoton cike yake da tunanin yakin cacar baki da yin fito na fito.

Rahotanni na cewa, a kwanan baya ne ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, ta mika rahotonta game da dabarun tsaron kasa ga majalisar dokokin kasar, wanda a ciki ya bayyana kasar Sin a matsayin babbar abokiyar hamayyar Amurka, da Rasha a matsayin babbar barazana.

Wang Wenbin ya kuma jaddada cewa, a halin da ake ciki yanzu, ya kamata dukkan bangarorin su kara karfafa gwiwa, da goyon bayan kasashen Rasha da Ukraine, don su ci gaba da tattaunawa, tare da samun sakamako, ta hanyar shawarwarin zaman lafiya. (Ibrahim)