logo

HAUSA

Medinski: Rasha ta karbi shawarwarin Ukrainian na kasancewa tsaka-tsaki da matsayi da bai shafi nukiliya ba

2022-03-29 21:20:42 CMG Hausa

A ranar 29 ga watan Maris, agogon kasar, jagoran tawagar kasar Rasha, Vladimir Medinsky, ya bayyana a ranar farko na zagaye na biyar na shawarwarin tsakanin kasashen Rasha da Ukraine cewa, kasar Rasha ta karbi rubutaccen shawarwari daga Ukraine, inda ta tabbatar da aniyarta ta ci gaba da kasancewa tsaka-tsaki, da matsayin da bai shafi nukuliya ba. Ya kuma bayyana cewa, kasar Rasha ba ta adawa da shigar kasar Ukraine cikin kungiyar Tarayyar Turai. (Ibrahim)