logo

HAUSA

Kungiyoyin al’ummun Sin sun bayar da ra’ayoyinsu kan kiyaye hakkin bil Adama

2022-03-29 10:39:22 CMG Hausa

 

Tun bayan an bude taro karo na 49 na kwamitin kula da hakkokin bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya, wasu kungiyoyin al’ummun kasar Sin sun halarci taron ta kafar bidiyo, inda suka bayar da ra’ayoyinsu, kan yadda za a kiyaye hakkin bil Adama yayin da ake fama da cutar COVID-19, da sa kaimi ga samun dawaumammen ci gaba, da kuma kara ba da kariya ga al’adun kananan kabilu.

Lin Songtian, shugaban kungiyar sada zumunta da ketare ta jama’ar Sin ya bayyana cewa, yadda za a yi kokari domin jama’ar wata kasa da na wata kasa su kara jin dadin rayuwa da tsaro, shi ne burin sha’anin hakkin bil Adama na duk duniya. Kuma Ko da yaushe kasar Sin na bin ka’idar mai da jama’a a gaban komai, kana ta cika alkawarinta na kawar da dukkan al’ummunta fiye da biliyan 1.4 daga kangin talauci, lamarin da ya sa ta kasance wata kasa wadda jama’arta suka fi jin dadin zaman rayuwa a duk fadin duniya. Mr. Lin ya kara da cewa, game da waccan kasa mafi sukuni a duniya, tana tsoma baki kan aikin kiyaye hakkin bil Adama na sauran kasashe ko wace rana, amma ba ta dora muhimmanci ko kadan kan yadda jama’arta fiye da miliyan daya ke mutuwa sakamakon cutar COVID-19. Kowa ya gane mene ne hakikanin halin da wannan kasa take ciki wajen kare hakkin bil Adama.

Bugu da kari kuma, wakili dan kabilar Ugyur daga kungiyar yin mu’amala da ketare ta kananan kabilun Sin, ya gabatar da yadda aka raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Xinjiang, da yaki da ta’addanci, da masu tsattsauran ra’ayi na jihar. Kana ya musunta jita-jitar da yammacin duniya ke yadawa bisa hakikanan abubuwa da kididdiga.

Ban da shi ma, wakilai daga kungiyar kiyaye al’adun Tibet ta Sin, da cibiyar nazarin ilmin Tibet ta Sin, sun ba da jawabai, inda suka gabatar da manyan nasarorin da jihar Tibet ta samu wajen kare kayayyakin al’adun da aka gada daga kaka-da- kakani, da ma ci gaban sha’anin raya dakunan nune-nunen kayayyakin tarihi.   (Kande Gao)