logo

HAUSA

Bai kamata a dauki ma’aunai biyu wajen daidaita batutuwa masu jawo hankalin duniya ba

2022-03-29 10:52:25 CMG Hausa

 

Bisa labarin da aka samu, an ce, yayin da shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas ya gana da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a kasarsa a ranar 27 ga wata bisa agogon wurin, ya jaddada cewa, ya kamata gwamnatin Biden ta cika alkawarin da ta yi wa Falasdinu, ciki har da alkawarin aiwatar da yarjejeniyar kafa kasashe biyu da dai sauransu.

Game da wannan batun, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya nuna cewa, bai kamata kasashen duniya su dauki ma’aunai iri biyu wajen daidaita batun Falasdinu da sauran batutuwa masu jawo hankalin duniya ba.

Wang Wenbin ya kara da cewa, “Ya kamata a nuna tausayawa ga ’yan gudun hijira na kasar Ukraine, amma ’yan gudun hijira daga Gabas ta Tsakiya, da Afirka, Latin Amurka ba su bukatar hakan? Lallai ba za a amince da irin wannan ma’aunai iri biyu ba. Lahanta al’ummar Ukraine laifi ne na yaki, amma ba za a hukunta wadanda suka hallaka fararen hula na tsohuwar Yugoslavia, da Afghanistan, da Iraki da Sham ba? Lallai ba za a yarda da irin wannan ma’aunai iri biyu ba. Kai farmaki kan Ukraine aiki ne na karya ka’idar girmama ikon mulkin kasa, amma kai wa tsohuwar Yugoslavia, da Afghanistan, da Iraki, da Sham hare-hare ne na aikin bin doka? Lallai ba za a amince da irin wannan ma’aunai iri biyu ba. Ana nanata muhimmancin daina keta ikon mulkin kasa a kan batun Ukraine, amma an jaddada yadda kiyaye hakkin bil Adama ya zarce kiyaye ikon kasa muhimmanci a kan batutuwan da suka shafi tsohuwar Yugoslavia, da Afghanistan, da Iraki, da Sham. Lallai ba za a yarda da irin wannan ma’aunai iri biyu ba.” (Kande Gao)