logo

HAUSA

An Kaddamar Da Gasar Fidda Gwani A Fannin Fasahohin Sana’a Tsakanin Kasashen BRICS

2022-03-29 14:46:16 CMG Hausa

Ma’aikatar ilmi ta kasar Sin, za ta jagoranci shirya gasar fid da gwani a fannin fasahohin sana’a a tsakanin kasashen BRICS, wato kasashen Brazil, Rasha, Indiya, Sin wato China, da Afirka ta Kudu wato South Africa, wadda za ta gudana tsakanin watan Maris zuwa na Nuwambar shekarar nan da muke ciki, a kokarin kara azama wajen zurfafa hadin gwiwa da yin mu’amala a tsakanin kasashen na BRICS ta fannin ba da ilmi, da kafa managartan dandalin gasanni mai halin musamman na koyar da sana'o'in dogaro da kai.

Gasar da za a gudanar a bana, gasa ce ta karon farko wadda kasar Sin ta shirya a matsayinta na shugaba, karkashin tsarin kasashen BRICS. Hukumomin gwamnatocin kasashen 5 na BRICS ne suka ba da jagora wajen kyautatawa da tsara gasanni, bisa halin da ake ciki a fannin koyar da sana'o'in dogaro da kai, da kuma albarkatunsu na shirya gasanni.

Za a yi takara a fannoni fiye da 20 cikin gasar, wadanda suka hada da kera manyan injuna na zamani, da tattalin arzikin zamani, da sabbin masana’antu da dai sauransu, a kokarin karfafa kwarewar malamai da dalibai da ke cikin kwalejojin koyar da sana'o'in dogaro da kai a kasashen 5, a fannonin yin kirkire-kirkire, da taimakawa juna, da shirya ayyuka da yin hadin gwiwar, da kyautata yin mu’amala da hadin gwiwa a tsakanin kwalejoji masu ruwa da tsaki da kamfanoni, da kuma kara azama kan horas da masu fasahohi managarta a kasashen 5, wadanda za su biya bukatun kasa da kasa. (Tasallah Yuan)