logo

HAUSA

Wasu mahara sun dasa nakiya kan layin dogo na Kaduna zuwa Abuja

2022-03-29 10:59:39 CMG Hausa

Rahotanni daga hukumomin tsaron Najeriya na cewa, wasu gungun ’yan bindiga sun dasa nakiya a kan layin dogon da ya ratsa Abuja, babban birnin tarayyar kasar zuwa jihar Kaduna, inda wani jirgin kasa dake bin layin ya taka nakiyar, kuma nan take ya goce daga layin, jim kadan kuma ’yan bindigar sun budewa jirgin wuta, lamarin da ya jikkata wasu daga fasinjojin dake cikin jirgin, ko da yake kawo yanzu ba a kai ga tantance irin barnar da harin ya haifar ba.

Yayin harin na jiya Litinin, rahotanni sun ce jirgin na dauke da daruruwan fasinjoji. Kuma hakan na zuwa ne ’yan kwanaki, bayan da wasu gungun ’yan bindigar suka kai hari cikin filin jirgin saman kasa da kasa dake jihar Kaduna.  (Saminu)