logo

HAUSA

Manyan shugabannin kasar Sin sun nuna juyayi ga wadanda suka rasu a hadarin jirgin sama

2022-03-28 19:50:05 CRI

 Da yammacin yau Litinin ne, ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya kira taro, don tattauna ayyuka a kwanaki na baya-bayan nan. Yayin bude taron, babban sakataren kwamitin kolin JKS kana shugaban kasar Xi Jinping ya ba shawarar cewa, ya kamata shugabannin dake halartar taro su tashi tsaye, inda suka yi shiru na dan lokaci, don nuna juyayi ga ‘yan uwansu wadanda suka rasu sakamakon hadarin jirgin sama mai lamba MU5735 a ran 21 ga watan nan. (Amina Xu)