logo

HAUSA

Sin da UNHCR sun samar da agajin jin kai ga Afghanistan

2022-03-28 11:13:40 CRI

An gudanar da bikin mika kayayyakin agajin jin kai a birnin Kabul, babban birnin kasar Afghanistan, wanda asusun samar da gudummawar hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa na kasar Sin da ma hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD(UNHCR) suka samar. Jakadan kasar Sin a Afghanistan Mr.Wang Yu da makaddashin wakiliyar UNHCR a kasar, Yumiko Takashima, sun halarci bikin, wanda aka yi a jiya Lahadi.

Jakadan kasar Sin a Afghanistan Mr.Wang Yu ya bayyana cewa, tun bayan da aka janye sojojin kasashen waje daga Afghanistan a watan Agustan bara, an shiga wani muhimmin mataki na wanzar da zaman lafiya a kasar.  Yanzu haka, Afghanistan na cikin mawuyacin hali ta fannin jin kai da ma tattalin arziki, wanda ke bukatar taimako daga kasa da kasa. Ya ce Kasar Sin na goyon bayan MDD ta kara taka muhimmiyar rawa a kan batun, tare da amsa kiran MDD na samar da agajin gaggawa ga Afghanistan, musamman ta hannun UNHCR da WFP. Baya ga haka, kai tsaye, kasar Sin ta samar da gudummawar abinci da magunguna da sauransu ga Afghanistan, ta kuma tura jiragen sama 36 don saye da dauko ‘ya’yan icen Pine daga kasar, matakin da ya samar mata da kudi dala sama da miliyan 22.

Daga nata bangaren, Madam Yumiko Takashima ta bayyana godiya game da yadda asusun samar da gudummawar hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa na kasar Sin ya samar da jari ga hukumar UNHCR da ma yadda kasar Sin take dada samar da agajin jin kai ga Afghanistan. Ta ce, faduwa ta zo daidai da zama, gudummawar da kasar Sin ta samar za ta samar da taimako na zahiri ga ‘yan gudun hijira da ma yaran makaranta sama da dubu 90 da ke cikin kasar Afghanistan.(Lubabatu)