logo

HAUSA

Yawan mutanen da zazzabin Lassa ya kashe a Najeriya ya karu zuwa 123

2022-03-28 10:31:33 CMG Hausa

Hukumar dakile cutuka masu yaduwa a Najeriya NCDC ta sanar a ranar Lahadi cewa, adadin mutanen da cutar zazzabin Lassa ta kashe a Najeriya ya karu zuwa 123 yayin da gwamnati ke ci gaba da daukar matakan dakile annobar a fadin kasar.

Sanarwar da NCDC ta fitar ya nuna cewa, jimillar mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar ta yammacin Afrika ya kai 659 tun daga watan Janairu.

A cewar hukumar ta NCDC, yawan mutuwar da aka samu sakamakon barkewar annobar zazzabin Lassa ya kai kashi 18.7 bisa 100.

Galibin mutanen da cutar ta fi shafa ’yan tsakanin shekaru 21 zuwa 30 ne, a cewar hukumar yaki da cutukan.

NCDC ta ce, ana daukar kwayoyin zazzabin Lassa ne a jikin dabbobi, nau’in wasu beraye, wadanda ake samu a shiyyar yammacin Afrika, sannan ta bukaci makwabtan kasashe da su zauna cikin shiri game da barazanar yaduwar cutar zazzabin Lassa.

Hukumar dakile cutukan ta ce, tana ci gaba da rarraba magunguna ga jihohi da cibiyoyin kula da marasa lafiya a matsayin matakan dakile yaduwar cutar a kasar. (Ahmad)