logo

HAUSA

An nuna juyayi ga wadanda suka rasu a hadarin jirgin saman MU 5735

2022-03-27 16:12:23 CRI

A yammancin yau Lahadi 27 ga wata, an nuna juyayi ga wadanda suka rasa rayuka a hadarin jirgin sama mai lamba MU5735 na kamfanin China Eastern Airlines wanda ya faru a ranar 21 ga watan Maris da muke ciki a filin da aka gano jirgin, inda mamban majalisar gudanarwar kasar Wang Yong ya halarci taron.

Yau da yamma, da misalin karfe biyu, an fara taron nuna juyayi, an yi fito, inda dukkanin ma’aikatan sashen daidaita hadarin jirgin saman MU5735 cikin gaggawa na kasar Sin da ma’aikatan ceto da sauran mutanen da abin ya shafa sun tsaya a gaban jirgin saman da ya fadi sun yi shiru har na mintoci 3 domin nuna alhini ga wadanda suka rasa rayuka yayin hadarin.

Kana iyalan wadanda suka rasu, su ma sun nuna alhininsu karkashin taimakon gwamnatin wurin da kungiyar aiki a wurare daban daban.

A halin yanzu, sashen daidaita hadarin cikin gaggawa yana ci gaba da gudanar da bincike kan kayayyakin jirgin saman da gawarwakin wadanda suka rasu da takardun da abin ya shafa, tare kuma da gudanar da bincike kan musabbabin aukuwar hadarin. (Jamila)