logo

HAUSA

Masana’antun Sin Sun Samu Karuwar Riba Da Kashi 5% Tsakanin Janairu Zuwa Fabrairu

2022-03-27 16:48:59 CMG Hausa


Alkaluman hukumar kididdigar kasar Sin NBS, sun nuna cewa, masana’antun kasar Sin sun samu karuwar ribarsu da kashi 5 bisa 100 a watanni biyun farko na shekarar 2022, yayin da ake fuskantar matsin lambar tsadar kudaden gudanarwa da karancin ciniki.

Manyan masana’antun kasar sun cimma nasarar samun ribar da takai yuan biliyan 1,157.56, kwatankwacin dala biliyan 182 tsakanin watan Janairu zuwa Fabrairun shekarar 2022.

Zhu Hong , kwararriyar jami’a a hukumar NBS, ta bayana cewa, ribar da masana’atun ke samu tana ci gaba da karuwa tun daga shekarar bara, sai dai akwai gagarumar barazanar da ake fuskanta na karin tsadar kayayyaki da masana’antun ke fuskanta, yayin da alkaluman ribar da na cinikinsu yake raguwa.

Ta ce har yanzu, ingancin da ake samu game da ribar manyan rukunin masana’antu bashi da tabbaci, kana karuwar yawan ribar kananan masana’antu da matsakaita ba ta da yawa.

Zhu ta ce, yayin da wadannan kamfanoni ke cigaba da fuskantar wahalhalu da kalubaloli, hukumar NBS zata cigaba da bada tabbacin samar da kayayyaki masu yawa a daidaitaccen farashi, domin rage tsadar kudaden gudanarwar kamfanonin, sannan za a aiwatar da wasu manufofi domin tallafawa masana’antun sarrafa kayayyaki, kamar rage kudaden haraji ga kananan masana’antu.(Ahmad)