logo

HAUSA

Shugaban Amurka ya sake yin sharhi kan takwaransa na Rasha

2022-03-27 16:53:14 CRI

Jiya Asabar shugaban kasar Amurka Joe Biden, ya sake yin sharhi kan takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin a kasar Poland, inda ya bayyana cewa, bai kamata Putin ya ci gaba da rike mulki ba, daga baya fadar White House ta musunta lamarin cikin gaggawa, kuma shugaban Rasha Putin shi ma ya mayar da martani cewa, bai dace Biden ya fadi haka ba, saboda al’ummun Rasha ne ke da ikon zaben shugaban kasarsu.

Shugaba Biden ya yi tsokacin ne yayin da yake gabatar da jawabi a Warsaw, fadar mulkin kasar Poland a jiya, daga baya nan take jami’in fadar White House ya musunta hakan, inda ya bayyana cewa, Biden ba ya nufin sauke shugaban Rasha daga mukaminsa.

Wannan rana kuma, gidan talabijin na FOX na Amurka, ya ruwaito ra’ayin tsohuwar jami’ar hukumar leken asiri ta ma’aikatar tsaron kasar Recekah Koffler cewa, Rasha ta fara zargin Amurka game da shirya makarkashiyar tunzura al’ummun Rasha domin sauya ikon mulkin kasar, yanzu haka tsokacin da Biden ya yi a fili ya gaskata tuhumar da Rashar ke yiwa gwamnatin Washington.

Game da tsokacin na Biden, sakataren watsa labarai na shugaban Rasha Dmitry Peskov ya nuna cewa, Biden ba shi da ikon tsai da kuduri kan batun ba, saboda al’ummun Rasha ne suka zabi shugaban kasarsu. (Jamila)