logo

HAUSA

Sojojin Najeriya sun dakile harin ‘yan bindiga a filin jirgin saman jihar Kaduna

2022-03-27 20:51:41 CRI

Dakarun sojojin Najeriya a jihar Kaduna dake arewa maso yammacin kasar, sun yi nasarar killace hanyar zuwa filin jirgin sama na kasa da kasa dake Kaduna, inda suka dakile harin da ‘yan bindiga suka kaddamar a cikin birnin, kamar yadda gwamnatin jihar ta bayyana.

A cewar Sameul Aruwan, kwamishinan al’amurran tsaron cikin gidan jihar Kaduna, sojojin sun mamaye filin jirgin saman, inda suka mayar da martanin gaggawa kan ‘yan bindigar tare da dakile yunkurin kai harin.

Wata majiyar sojoji, ta shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, sama da ‘yan bindigar 200 ne suka shirya kai harin, lamarin da ya yi sanadiyyar kashe wani jami’in hukumar kula da sararin saman Najeriya, wanda ya kwarmata bayanan gano maharan.(Ahmad)