logo

HAUSA

Kamfanin kasar Sin ya kaddamar da ginin hanya a Ghana

2022-03-26 20:34:56 CMG Hausa

 

Kamfanin Sinohydro na kasar Sin, ya kaddamar da ginin wata hanya a cibiyar Kumasi, birni mafi girma na biyu a kasar Ghana a jiya Juma’a.

Aikin hanyar mai tsawon kilomita 100, ya kunshi ginin magudanan ruwa da tubali da shimfidar hanyar mai inganci, wanda ake sa ran zai inganta tsarin hanyoyin birnin da saukaka zirga-zirga.

Da yake jawabi yayin bikin kaddamar da aikin, mataimakin shugaban kasar Ghana, Mahamudu Bawumia ya bayyana farin cikin ganin za a fara aikin hanyar ta birnin Kumasi a kan lokaci.

Shi kuwa jakadan kasar Sin a Ghana Lu Kun, yabawa injiniyoyin Ghana da takwarorinsu Sinawa ya yi bisa tsaya da suka yi kan aikin da yin kyakkyawan shirin fara shi, duk da kalubalen annobar COVID-19. (Fa’iza Mustapha)