logo

HAUSA

Jakadan Sin dake Nijeriya ya gana da tawagar hukumar IAEA

2022-03-26 16:34:17 CRI

Jakadan kasar Sin dake kasar Nijeriya Cui Jianchun, ya gana da shugaban sashen Afirka na ofishin kula da harkokin yin hadin gwiwa ta fuskar fasaha ta hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, Shaukat Abdulrazak, da shugaban kwamitin kula da harkokin makamashin nukiliya na Nijeriya Yusuf Aminu Ahmed, inda bangarorin uku suka tattauna kan yadda za a yi amfani da makamashin nukiliya cikin lumana.

Shaukat Abdulrazak ya bayyana cewa, Sin babbar kasa ce dake amfani da makamashi da fasahohin nukiliya, wadda ta samu manyan nasarori a wannan fanni a goman shekaru da suka gabata, tare da samun fasahohi da dama. Don haka, yana son hada hannu da kasar Sin don taimakawa kasashen Afirka wajen amfani da fasahohin nukiliya a fannonin kiwon lafiya, da kiyaye muhalli, da nazari da sauransu, karkashin tsarin hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa da taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka.

A nasa bangare, Yusuf Aminu Ahmed ya yi bayani game da yanayin ci gaban sha’anin makamashin nukiliya na Nijeriya, yana mai cewa, amfani da makamashin nukiliya cikin lumana zai sassauta matsalar makamashi mai tsanani a kasar, kana zai taimaka wajen kafa tsarin amfani da fasahohin nukiliya don amfanawa kasar da jama’arta. Har ila yau, ya ce Nijeriya tana son kara hadin gwiwa da kasar Sin da hukumar IAEA don sa kaimi ga samun ci gaban fasahohin nukiliya a kasar.

Shi kuwa a nasa bangaren, jakada Cui ya bayyana cewa, a matsayin kasar da ta fi kowacce yawan jama’a kuma mafi samun ci gaban tattalin arziki a nahiyar Afirka, Nijeriya tana da kyakkyawar makomar kasuwa, kuma Sin tana son hadin gwiwa da hukumar IAEA da kwamitin kula da harkokin makamashin nukiliya na kasar Nijeriya, don musayar fasahohi da amfanawa jama’ar kasar. (Zainab)