logo

HAUSA

Hukumar kwadago ta duniya ta zabi sabon shugaba

2022-03-26 16:03:50 CMG Hausa

 

Hukumar kwadago ta duniya ILO, ta sanar da Gilbert F. Houngbo na kasar Togo, a matsayin sabon Darakta Janar mai jiran gado.

Hukumar gudanarwar MDD, wadda ta kunshi wakilan gwamnatoci da ma’aikata ce ta zabe shi, yayin wani taron da aka yi jiya Juma’a a Geneva.

Gilbert F. Houngbo, tsohon firaministan Togo, zai zama shugaban hukumar na 11, kuma dan Afrika na farko da zai rike mukamin.

Wa’adin mulkinsa na shekaru 5 zai fara ne daga 1 ga watan Oktoban bana. Inda zai maye gurbin darakta janar mai ci, wato Guy Ryder na kasar Birtaniya, wanda ya kasance kan mukamin tun daga shekarar 2012.

Wasu ‘yan takara 4 daga kasashen Korea ta Kudu da Afrika ta Kudu da Faransa da Australia, su ma sun shiga takarar neman kujerar ta darakta janar na hukumar ta ILO.

Manufar hukumar ILO mai kasashe mambobi 187, wadda aka kafa a shekarar 1919 ita ce, inganta kyakkyawan yanayin aiki ga kowa. (Fa’iza Mustapha)