logo

HAUSA

Kasar Sin na maraba da duk wani mataki da nufin kawar da matsalar jin kai a Ukraine

2022-03-25 09:57:20 CMG Hausa

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya bayyana a jiya Alhamis cewa, kasarsa na maraba da duk wani shiri da ma matakin da za su taimaka, wajen shawo kan matsalar jin kai da ake fuskanta a kasar Ukraine.

Zhang Jun ya shaidawa zaman taron gaggawa na babban zauren MDD kan Ukraine cewa, muhimmin batu da kasar Sin ke son gabatarwa, shi ne sa kaimi ga al'ummomin kasa da kasa da MDD, su mai da hankali kan yanayin jin kai a Ukraine.

Zhang ya kara da cewa, kasar Sin ta bukaci bangarorin da abin ya shafa, da su karfafa hadin gwiwa kan batun jin kai, da kare lafiyar fararen hula yadda ya kamata, musamman ma masu rauni, kamar mata da kananan yara, da saukaka aikin kwashe ma'aikata da ayyukan jin kai. (Ibrahim)