logo

HAUSA

Shugabannin Afirka sun himmatu wajen magance laifukan da ake aikatawa ta yanar gizo

2022-03-25 09:44:44 CMG Hausa

Jiya ne, aka kammala taron yini biyu, na shugabannin kasashen Afirka kan harkokin tsaro ta intanet, tare da amincewa da sanarwar nahiyar game da harkokin tsaron yanar gizo, da yaki da laifufukan da ake aikatawa ta intanet a nahiyar Afirka.

Manufar taron shugabannin kasashen Afirka kan tsaron intanet na yini biyu, wanda hukumar kula da tattalin arzikin Afirka ta MDD (ECA) a takaice tare da hadin gwiwar gwamnatin kasar Togo suka shirya, ita ce tantance yanayin tsaron yanar gizo, da kuma gabatar da shawarwarin siyasa ga gwamnatocin Afrika.

A jawabinsa yayin taron, shugaban kasar Togo, Faure Essozimna Gnassingbe, ya shaidawa taron kolin game da bukatar yin hadin gwiwa don yaki da aikata laifuka a zamanin da duniya ta karkata ga amfani da yanar gizo, yanayin da a cewar hukumar UNECA, ya samar da dimbin damammaki masu ban mamaki ga bil-adama.

Ya kuma bukaci ragowar kasashen Afirka, da su amince da yarjejeniyar tsaro ta yanar gizo da kare bayanan sirri ta kungiyar Tarayyar Afirka (AU) da aka amince da ita a Malabo na kasar Equatorial Guinea a watan Yunin shekarar 2014. (Ibrahim Yaya)