logo

HAUSA

Shugaba Xi ya zanta da firaministan Birtaniya

2022-03-25 20:18:37 CMG Hausa

 

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta da firaministan Birtaniya Boris Johnson ta wayar tarho da yammacin Juma’ar nan.

Yayin tattaunawar ta su, shugaba Xi ya ce a bana an cika shekaru 50, da kafa huldar jakadanci tsakanin Sin da Birtaniya. Kuma cikin wadannan shekaru, sassan biyu sun fadada hada-hadar cinikayya, daga kudin da suka kai dala miliyan 300 zuwa dala biliyan 100. Kaza lika yawan jarin da suke zuba wa juna ya daga, zuwa kusan dala biliyan 50. Inda birnin London ya zamo babbar cibiyar hada-hadar kudaden RMB na Sin.

Xi ya kara da cewa, Sin da Birtaniya na da yanayi mabambanta, da kuma salon ci gaba daban daban. Amma duk da haka, ya dace kasashen biyu su mayar da hankali, ga ci gaba mai dorewa na dogon lokaci, su martaba juna, tare da ingiza shawarwari da musaya, tare da fadada hadin gwiwar su bisa tushen rungumar juna.

A nasa bangare kuwa, Boris Johnson cewa ya yi alakar Birtaniya da Sin, na da matukar muhimmanci. Kuma Birtaniya a shirye take ta zanta da Sin, tare da karfafa musaya da hadin gwiwa, da fadada hadin gwiwar raya tattalin arziki da cinikayya, da zurfafa tattaunawa kan batutuwan da suka shafi duniya baki daya, da kuma na shiyya-shiyya, musamman ma batutuwan irin su sauyin yanayi, da fadada amfani da makamashin tsirrai.    (Saminu)