logo

HAUSA

Sin tana maraba da matakin Habasha na dakatar da yaki a cikin kasar

2022-03-25 20:28:42 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, a kwanakin baya, gwamnatin kasar Habasha ta sanar da dakatar da yaki nan take, don tabbatar da shigar da kayayyakin jin kai zuwa jihar Tigray dake kasar, ta yadda za a kyautata yanayin jin kai a jihar, kuma Sin ta yi maraba da wannan mataki na Habasha.

Wang Wenbin ya bayyana cewa, Sin tana goyon bayan bangarori daban daban na Habasha, bisa burin su na warware matsaloli, da kwantar da hankali, da kuma yin sulhu ta hanyar yin shawarwari. Kana tana fatan Habasha za ta samu zaman lafiya da wadata.

Sin ta riga ta samar da gudummawar jin kai, kamar kayan abinci, da alluran rigakafin cutar COVID-19 ga Habasha, don sassauta yanayin jin kai a kasar. A nan gaba kuma, Sin za ta ci gaba da samar da gudummawar jin kai ga Habasha ciki har da jihar Tigray, don taimakawa wajen sa kaimi ga samun zaman lafiya da karko, da kuma bunkasuwa a yankin. (Zainab)